A cewar rahoton rukunin fassara na Ofishin Yada Labaran Hauza, Hujjatul Islam wal-Muslimin Sayyid Ahmad Ali Abedi, limamin juma'a na Mumbai, wanda shi ne wakilin Ayatullah Sayyid Ali Sistani a Indiya, a cikin wata sanarwa, ya bayyana baƙin ciki da tsananin damuwarsa game da abubuwan da suka faru na baya-bayan nan a Iran, ya kuma jaddada cewa duk wani makirci da ƙasashe masu mulkin mallaka da munafukan yaransu suka yi a kan jagorancin juyin juya halin Musulunci da kuma manyan maraji'an Shi'a, ya ci tura, kuma nan gaba ma za su ci tura.
Ya ci gaba da cewa: "Yanayin da Iran ke ciki a halin yanzu yana da matukar ciwo da bakin ciki. Rahotannin da aka yada game da mutanen da suka yi shahada suna haifar da bakin ciki ga kowane mutum mai 'yanci. Cike da matukar nadama, dole ne a ce waɗannan ƴan ƙasar Iran da aka zalunta an kashe su ne ta hannun munafukai."
Wannan babban malami na Indiya ya kara da cewa: "Tun daga farkon nasarar juyin juya halin Musulunci, ƙasashe masu mulkin mallaka, musamman Amurka da kawayenta, ba su taɓa son su ga wannan tsarin Musulunci ya yi nasara ba. Sun yi amfani da takunkumi daban-daban bisa dalilai iri-iri, kuma ta kowace hanya sun yi ƙoƙari su raunana ko kuma rushe wannan tsarin, amma a kowane mataki suna cin karo da gazawa."
Limamin juma'a na Mumbai ya bayyana cewa: "Babban dalilin wannan gazawar shi ne, Iran tun daga farko tana ƙarƙashin kulawa da kuma kariyar shugaban Imamuz zaman (Ajtfs), kuma har yanzu wannan tallafin yana ci gaba gaba ɗaya. Ko da yake abubuwan da suka faru na baya-bayan nan suna da ɗaci da damuwa, amma gaskiyar da take fitowa fili ita ce, munafukai da maƙiyan Musulunci an tsara sune don neman raunana gwamnatin Musulunci."
Ya ci gaba da cewa: "Da shudewar lokaci, labulen asiri za su buɗe, kuma kowa zai fahimci irin tsattsauran makirci da tsare-tsare da ke bayan waɗannan al'amura, da kuma cewa da yawa daga cikin waɗanda suke amsa sunayen ƴan Iran, a haƙiƙa ba su da alaƙa ta gaske da Iran da al'ummar Iran."
Hujjatul Islam Ahmad Abedi ya ci gaba da jaddadawa cewa: "Tushen juyin juya halin Musulunci tun daga farko ya ta'allaka ne akan marja'iyya da kakkarfan jagoranci. Maraja'ai suna da matsayi mai zurfi a cikin zukatan ƴan Shi'a, kuma kowane ɗan Shi'a da dukan rayuwarsa yana da alaƙa da su kuma yana girmama su; domin ana ɗaukar manyan maraji'an a matsayin wakilan gidan Annabi (A.S.). Saboda haka, duk wani katsalandan ga wannan matsayi mai tsarki ba zai yuwu a karɓa ba."
Ya kara da cewa: "Idan a yau Iran ta tsira daga manyan haɗarurruka da dama, babban dalilin haka shi ne basirar jagoranci, hikima da hangen nesa na jagoran juyin juya halin Musulunci. Wannan jagoranci ne ya ceci Iran daga cikin laka ta maƙarƙashiya, kuma ya ba da amsa mai ƙarfi da kakkausan murya ga ƙasashe masu mulkin mallaka."
Muna roƙon Allah Maɗaukaki, ya kiyaye jagoran juyin juya halin Musulunci, ya ba shi dogon rayuwa mai daraja da lafiya, Musulunci da al'ummar Musulunci su ci gaba da cin moriyar sa, ya halaka maƙiyan Musulunci, kuma ya tabbatar da wannan tsarin Musulunci mai tsarki har zuwa tashin Alkiyama.
Your Comment